12 Maris 2015 - 11:02
Sojojin Iraki sun 'yanto garin Takrit

Sojin Irakin sun samu nasarar 'yanto gari mafi muhimmanci daga hannun 'yan ta'adda na Da'ish

kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna- ya rawaito cewa, gidan talabijin na Al'sumari ya bada sanarwar 'yanto gari mafi muhimmanci a yankin Salahuddin na Iraki, sojin Iraki tare da hadin gwiwar sojin sa kai sun samu nasarar kwato garin Takrit wanda ya jima a hannun 'yan ta'adda na Da'ish kuma a zaman yanzu garin yana hannun sojojin kwamnati.ABNA